Taron da bangaren gwamnatin tarayya da na shugabannin kungiyar malaman jami’o’i su ka gudanar a jiya Litinin ya ci tura, domin sun kasa cimma matsayar da za a kawo karshen yajin aikin da malaman suka fara tun a ranar 4 Ga Nuwamba, 2018.
Wannan ne zama na shida tun bayan fara yajin aikin.
Bayan kammala taron da aka yi a hedikwatar Ma’aikatar Kwadago da Ingantuwar Ayyuka, Minista Chris Ngige ya fito ya shaida wa manema labarai cewa har yanzu ba a cimma matsaya ba, kuma za a sake zaunawa kamar yadda kungiyar ta nema.
Da aka tambaye shi batun naira bilyan 50 da ASUU ta ce su ta ke so ta fara gani a kasa tukunna kafin ta yarda ta janye daga yajin aiki, sai Ngige ya ce ai gwamnati ta ma ciro naira bilyan 167 daga asusun TETFund ba milyan 50 ake magana ba.
“Amma batun biya sai dai a kai a kai, domin akwai wasu basussukan tun na 2009, wasu kuma tun na 2012. Kuma har mun fara sakin naira bilyan 15.400, domin biyan cabin inda aka samu akasin kudaden albashi.”
Sai dai kuma shugaban ASUU Biodun Ogunbiyi, ya ce ba za su janye yajinn aiki ba, amma za a sake zama, domin akwai babban batun da ake magana a kai, kuma shi ne har yau dai gwamnati ke kokarin ta waske daga gare shi.
Ogunbiyi ya ce ASUU ta na magana a kan batun kudin farfado da tsarin ilmi kacokan, wanda ta ce sai ta ga gwamnati ta fara ware naira bilyan 50 domin soma aiki, don a ga cewa gwamnati da gaske ta ke yi.
Ya ce amma ba cewa suka yi sai gwamnati ta ware wa malaman jami’o’i naira bilyan 50 ba.
Duk da cewa a ranar Lahadi Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci jami’an gwamnati da za zauna da kungiyar ASUU a yi ta ta kare, hakan bai yiwu ba, bayan zaman da bangarorin biyu suka yi a jiya Litinin da yamma.
ASALIN TIRKA-TIRKAR
Cikin shekarar 2013, an rattaba yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASSU cewa gwamnati za ta ware naira tiriliyan 1.3 domin a farfado da ilmin manyan makarantu na jami’o’i.
An rattaba cewa za a fitar da naira bilyan 220 a cikin 2013 domin a fara aiki da su. Daga nan kuma a cikin 2014 za a fitar da naira bilyan 220, haka ma a 2015, 2016 da 2017 za a rika fitar da bilyan 220 ana aiki da su.
To, tun da aka fitar da naira bilyan 220 na farko a zamanin Goodluck Jonathan aka fara aiki da su, har yau ba a sake fitar da ko sisi an ci gaba da ayyukan ba.