Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin Kungiyar Daliban Jami’a, NANS, inda suka tattauna batun matsalar da ta dabaibaye fannin ilmi a kasar nan.
Sun gana ne inda ya ba su bayanin kokarin sasantawa da Malaman Jami’a da ake yi, wadanda suka fara yajin aiki tun a ranar 4 Ga nuwamba, 2018.
Buhari ya shaida musu cewa karyewar farashin danyen man fetur na daga cikin dalilan da suka sa ba za a iya biya wa Malaman Jami’o’i dukkan bukatun da suka nema a biya musu ba.
Haka daya daga cikin ‘yan tawagar daliban da ya je daga Jami’ar Abuja ya shaida wa manema labarai bayan ganawar su da Buhari a Fadar Shugaban Kasa a jiya Alhamis.
Su ma shugabannin manyan Kwalejojin Fasaha na Kasa sun shiga yajin aiki a ranar 23 Ga Disamba.
Kasa samun wannan daidaito ne ya sa dalibai su ka yi barazanar yi wa Gwamnatin Tarayya da malaman jami’o’i bore a ranar 7 Ga Janairu, a bisa dalilin cewa sun gaji da zaman gida haka nan. Wannan ne ya sa Buhari ya kira su taron ganawa.
Dalibin mai suna Yahuza ya ce Buhari ya shaida musu cewa akwai fannoni da dama wadanda gwamnati ba za ta iya biyan dukkan bukatun su ba.
Ya ce Buhari ya ce kuma ba fannin ilimi ne kadai fannonin da suka wajaba gwamnati ta kula da su ba.