Yadda Babangida ya raba kan Atiku da Obasanjo -TY Danjuma

0

Tsohon Babban Hafsan Dakarun Najeriya, TY Danjuma, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Kasa Ibrahim Babangida ne ya haddasa rabuwar kawuna a tsakanin Olusegun Obasanjo da Atiku Abubakar a lokacin da suke mulki a matsayin shugaba da mataimaki tsakanin 1999 zuwa 2003.

Haka Danjuma ya bayyana a wurin wani taro a ranar 25 Ga Oktoba, 2002, wanda ya yi tare da Jakadan Amurka a Najeriya na lokacin Howard Jeter, a Abuja.

Kafar yada labaran tonon silili ta Wikileaks ce ta tona wannan taron sirrin kuma ta buga a shafin ta na intanet.

An yi wancan taro na sirri a tsakanin mutanen biyu a lokacin da Atiku ya rika kakudubar neman fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2003, a daya bangare kuma Obasanjo na fuskantar yunkurin tsigewa daga Majalisar Tarayya a karkashin jagorancin Kakakin Majalisa na lokacin Ghali Umar Na-Abba.

Danjuma wanda a lokacin shi ne Ministan Tsaro, ya ce Babangida ya rika kulla tuggu da kutunguilar yadda zai kawo farraka tsakanin Obasanjo da kuma Atku.

Ya ce Babangida ya shawarci Obasanjo ya watsar da Atiku ya kama wani a matsayin mataimaki daga Arewa, domin ya kara wa kan sa kima da mutunci a Arewa.

“Bayan da Babangida ya kasa shawo kan Obasanjo ya watsar da Atiku har tsawon watanni tara, sai kuma ya sake shigo wa Atiku da wata dabarar.

“Danjuma ya kara da cewa: Daga nan sai Babangida ya ribbaci Atiku, ya ja shi a jika. Shi kuma Atiku idon sa ya rufe cewa Babangida ne kore shi daga aiki kwastan, saboda an danganta shi da mu’amala da wasu gaggan masu safarar kwaya. Sai ya bi Babangida ya rika yi masa hudubar-shaidan.”

Danjuma ya kara da cewa Atiku sai ya kitsa tuggun da kafafen yada labarai suka rika yayatawa cewa Obasanjo ya sauka daga mulki, domin a kara karfafa nagartar dimokradiyya a Najeriya.

“Danjuma ya fahimci wannan tuggun ya na neman biya wa Babangida bukatar sa kenan. Wato idan Atiku ya shiga takara, to fa tilas Obasanjo zai fito da makudan kudade ya kashe kenan domin ya samu tikitin tsayawa takara a karkashin PDP, idan aka wancakalar da Atiku.

Dama kuma sati daya kafin Danjuma ya gana da Jakadan Amurka a Najariya, sai da shi jakadan ya yi ganawar sirri ta tsawon mintina 90 da Atiku Abubakar a gidan shi Atiku. Sun yi ganawar sirrin a ranar 16 Ga Oktoba, 2002.

“An kuma fallasa wani taro da aka yi inda Atiku ya ce masa shi da Obasanjo ba su yi wata kwakkwarar mu’amala ba kafin 1998 ana kusa ga yin zaben 1999.

“Sun hadu ne ta dalilin Shehu ‘Yar’Adua, wanda shi ne mataimaki a lokacin da Obasanjo ke shugaban kasa na mulkin soja. ‘Yar-Adua bayan yin ritaya ya kafa jam’iyyar PDM, amma ya mutu a lokacin da ya ke tsare a karkashin gwamnatin Sani Abacha.

Rahoton ya kuma fallasa yadda su Babangida suka kulla yadda Obasanjo ya zama shugaban kasa a zaben 1999. Ya kuma fallasa yadda shugaban lokacin Abdulsalami Abubakar ya rubuta takardar yafe wa Obasanjo laifin sa, amma sai ya rubuta wata rana can ta baya da nisa, domin ya samu damar tsakaya takarar shugaban kasa har ya zama shi ne shugaba.

Cikin wadanda aka yi zargin sun kara rura wutar fitina har da tsohon dan siyasa kuma wanda aka rika yi wa kallon gogarman tuggun siyasa, wato marigayi Tony Anenih.

“An ce Atiku ya cika da mamaki yadda bayan isar sa Amurka ya ji labarin wanda Obasanjo ya daure gindin ya zama shugaban majalisar dattawa, alhali shi da Obasanjo din sun amince da cewa ga wanda za a daure wa gindi ya zama shugaban majalisar ta dattawa.

An ce Atiku ya ce ya san hakan za ta iya faruwa, kuma ya yi zargin a cikin tuggun akwai hannun su gogaraman dan tuggu, Tony Amenih.

An kuma ce Atiku ya aika wa makusantan Obasanjo cewa idan suka sake zagaye shi su ka yi abin da ran su ke so, to za su sha kaye a wurin zaben fidda-gwani.

“Atiku ya rika bugun kirjin cewa ya na da goyon bayan mafi yawan gwamnaonin PDP na lokacin, mambobin kwamitin zartaswa na PDP da kuma mafi yawan ‘yan majalisar tarayya.

Obasanjo dai da Atiku sun kasance manyan abokan gabar juna, har zuwa kusan karshen 2018, lokacin da Obasanjo ya dawo daga rakiyar Buhari, ya ce a zabi Atuku a zaben 2019.

Share.

game da Author