Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta yi kira ga gwamnatocin duniya da su rika ware isassun kudade domin inganta kiwon lafiyar mutanen kasashen su.
Bill da Melinda Gates sun yi wannan kira ne a makon da ya gabata inda suka bayyana cewa yin haka zai taimaka wajen kawar da matsalolin da duniya ke fama da su a fanin kiwon lafiya.
” Bincike ya nuna cewa kiwon lafiyar mutanen dake fama da talauci a kasashen su ya yi matukar raguwa a dalilin maida hakalin da gwamnatocin kasashen ke yi wajen samarwa mutanenta kiwon lafiya mai nagarta.
” A dalilin haka muke kira ga kasashen duniya musamman kasashen dake tasowa da su kara ware kudade domin fannin kiwon lafiyar kasashen su.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne gidauniyyar Bill da Melinda Gates ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kara yawan kudaden da take ware wa fannin kiwon lafiyar kasar domin samar da kiwon lafiya mai nagarta ga mutanen kasar.
Gudauniyyar ta yi wannan kira ne a taron inganta hanyoyin samar da dabarun bada tazarar iyali da cibiyar DRPC ta shirya sannan ta gudanar babban birnin tarayya, Abuja.
Jami’ar gidauniyyar Paulin Basinga ta bayyana cewa yin hakan zai taimaka wajen karkato da hankalin gwamnatin kasar wajen inganta kiwon lafiyar mutane da hana kasar yawan dogaro da tallafin da take samu daga kasashen waje musamman yanzu da suka fara janye tallafin.
A dalilin irin haka ne cikin irin gudunmawar da Najeriya kan samu daga kungiyoyin duniya Jami’in kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Wondimagegnehu Alemu ya bayyana cewa kungiyar ta ware dala miliyan 178 domin tallafawa Najeriya wajen kawar da wasu cututtuka har na tsawon shekaru biyu.
A bayanan da ya yi Alemu ya ce za a kashe dala miliyan 127 wurin kawar da cutar shan inna, Za kuma a kashe dala miliyan 30 wajen kawar da cututtukan da aka fi kamuwa da su a kasar kamar su zazzabin cizon sauro, tarin fuka da cutar Kanjamau.
Ya kuma kara da cewa dala miliyan 8.1 kuwa za a kashe su wajen inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana sannan da dabarun bada tazarar haihuwa sannan sauran kudaden za a yi amfani da su ne wajen hana bullowar cututtuka a kasar.
Discussion about this post