Wani helikwafta ya rikito yayin kai harin bama-bamai kan Boko Haram

0

Wani jirgin yaki samfurin helikwafta ya rikito kasa, a daidai lokacin da ya ke kai harin bama-bamai a kan Boko Haram.

An kara samun tabbacin wannan fadowa da helikwaftan ya yi daga bakin Kakakin Rundunar Sojojin Sama, Air Commodore Ibikunle Daramola.

Sai dai kuma Daramola ya ce babu takamaimen na musabbabin fadowar jirgin kasa, kasancewa an san sun mallaki manyan bindigogin tashi-gari-gari-barde, da ake harbor jirage da su.

Amma kuma akwai yiwuwar cewa watakila Boko Haram ne suka harbo jirgin.

“An samu labarin bacewar wani helikwafta mallakar Rundunar Sojoji Saman Najeriya (NAF), yayin da ke kai harin kai daukin taimaka wa Sojojin Bataliya ta 145 a Damasak, Arewacin Jihar Barno.” Inji Daramola.

Ya ce jirgin ya bace da misalign karfe 7:45 na ranar Laraba, 2 Ga Janairu, 2019.

Share.

game da Author