Dan wasan Super Eagles mai buga wa Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea da ke London, Victor Moses, ya koma kungiyar Fenerbace da ke Turkiyya.
Chelsea ce ta bada lamunin sa a can, inda zai shafe watanni 18 har zuwa karshen kakar wasa ta 2019/2020.
An bada lamunin sa a can ne saboda ya kasa shiga cikin kwararrun ‘yan wasan da mai horas da ‘yan wasan Chelsea, Mauzirio Sarri ke bukatar su rika taka leda a sabon salon wasan da ya shigo wa Chelsea da shi.
A lokacin tsohon kociya Antonio Conte, Moses ba shi da matsala, domin ana yawan sa shi wasa, kasancewa Chelsea na buga salon 3-4-3 ne.
Sai dai kuma a yanzu sabon kociya Sarri ya shigo da salon 4-3-3, wanda tun da ya zo. Sau biyar kadai ya sa Moses wasa.