Hukumar Tara Kudaden Haraji na Cikin Gida, wato FIRS, ta bayyana tara zunzurutun kudade har naira tiriliyan 5. A cikin shekarar 2018 da ta gabata.
FIRS ta ce a tarihin Najeriya ba a taba tara wadannan makudan kudade a cikin shekara daya ba, sai a cikin 2018 da ta gabata.
Shugaban Hukumar, Tunde Fowler ne ya bayyana haka a Lagos, a lokacin da ya ke jawabi wurin wani taro kan sha’anin kudaden haraji a Lagos.
A jiya Litinin din ne kuma a wurin taron ya ce Najeriya ta kudiri aniyar tara har naira tiriliyan 8 a cikin shekarar 2019 da mu ke ciki.
Sai dai kuma za a iya cewa Fowler ya yi baki-biyu kenan, domin a wurin taron kasafta kudaden gwamnatin tarayya a cikin watan Disamba, ya bayyana cewa FIRS ta tara naira tiriliyan 4.63 ya zuwa watan Nuwamba, a cikin 2018.
Amma kuma da ya ke jawabi a Lagos, ya ce an tara naira tiriliyan 5.32, wanda ya ce sun zarta na naira tiriliyan 5.07 da aka taba tarawa cikin 2012, a lokacin gwamnatin PDP.
Fowler ya ce an tara harajin naira tiriliyan 2.467 daga harajin da ba na harkoki danyen mai ba. sai kuma naira tiriliyan 2.95 daga kudaden shiga na harkokin mai.
Discussion about this post