Tsohon gwamman jihar Kano Hamza Abdullahi ya rasu a wani asibiti a Kasar Jamus bayan fama da yayi da rashin lafiya.
Marigayi Hamza Abdullahi ya rasu ya na da shekara 74 a duniya.
Kakakin masarautar Hadejia, Talaki Mohammad da ya sanar da rasuwar Marigayi Hamza ya bayyana cewa masarautar na juyayin rasuwar Hamza.
Bayan gwamnan Kano da ya rike a lokacin mulkin Janar Muhammadu Buhari, ya yi ministan Ayyuka da Gidaje da kuma ministan Babban Birnin Tarayya Abuja a lokacin mulkin Ibrahim Babangida.