Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya kalubalanci dattawan Arewa su fito su na yi wa gwamnati kururuwar kukan rashin tsaro, kamar yadda suka rika yi a zamanin gwamnatin Jonathan da ta shude.
Dogara ya bayyana haka a Lafiya Jihar Nasarawa, a lokacin yakin neman zaben PDP a Lafiya a ranar Alhamis da ta gabata.
Dogara ya ce ba daidai ba ne a ce dattawan da suke babatun matsalar rashin tsaro a lokacin Jonathan, yanzu kuma su kame bakin su su yi shiru, matsalar sai kara tabarbarewa ta ke yi a Arewa.
Ya yi tir da wasu masu halin tumasancin da suka maida wasu shugabanni kamar wasu dodanni.
Dogara ya kara yin kira ga ‘yan Najeriya da su tashi tsaye su ceto kasar nan daga mummunar matsalar tsaro.
“Kamar yadda na furta a wurin kamfen a Gombe, zaben 2019 ba magana ba ce tsakanin Buhari da Atiku. Zabe ne a kan neman kawar da matsalar tsaro da kuma yunwa.
Dogara ya yi tsokaci a kan matsalar tsaro a Barno, hanyar Abuja zuwa Kaduna, Zamfara, Katsina, Nasarawa, Benue, Filato da kuma Sokoto.
“Saboda abin ma ya yi yawa, har ba zan iya ambaton sauran jihohi da garuruwan da matsalar ta shafa ba.
“Kiri-kiri a lokacin Jonathan dattawan Barno suka rika babatu, amma kuma yanzu sun yi shiru.
Shin ina dattawan barno din ne a yanzu? Kuma ina dattawan Arewa ne?” Inji Dogara.