TSAKANIN ONNOGHEN DA CCT: Yadda gardandami ya barke tsakanin lauyan gwamnati da lauyan Onnoghen

0

Babban Mai Shari’a na Kasa, Walter Onnoghen bai halarci zaman kotun da aka kai shi kara a yau Litini ba a kotun CCT. Sai dai kuma lauyoyi 46 sun wakilce shi, wadanda a cikin su, da dama duk manyan lauyoyi ne na gidi, wato SAN.

Babban Lauya Wale Olanipekun ne jagoran rundunar lauyoyin da ke kare Onnaghen. Sauran kuma har da Kanu Agabi, Adegboga Awomolo, Chris Uche da sauran su.

Zaman shari’a ce ake neman fara yi, ta babban alkalin Najeriya, wanda gwamnatin Buhari ta zarge shi da laifin kin bayyana kadarorin da ya mallaka.

Walter Onnoghen shi ne Babban Alkalin Najeriya na 17, kuma shi ne na farko da aka taba gurfanarwa a gaban shari’a.

Sai dai kuma a bisa dukkan alamu, ya bi shawarar gwamnonin yankin Kudu maso Gabas, da suka ce kada ya je kotun.

Daga cikin tankiyar abin da ya daure kai dangane da karar sa da gwamnati ta shigar, shi ne yadda aka yi abin a cikin gaggawa.

An yi zargin cewa wani tsohon hadimin Shugaba Buhari ne mai suna Dennis Aghanya, ya kai kwarmaton Onnonghen a rubuce, aka aika masa takardar neman bayyana kotu, kwana daya bayan mika takardar korafin da aka yi a akn sa.

Onnonghen, wanda aka rantsar a matsayin Babban Mai Shari’a cikin Maris, 2017, dan jihar Cross River ne.

KAKA-TSARA-KAKA:

Lauyoyin wanda ake kara sun cika kotun makil, haka bangaren gwamnati na masu gabatar da kara na wurin.

Babban Lauya na Gidi, wato SAN, Aliyu Umar, shi ne babban lauyan gwamnati mai gabatar da kara.

Daidai karfe 10:08 ne Mai Shari’a Danladi Umar ya kira karar da aka shigar kan Walter Onnaghen, amma shiru bai halarta ba, sai dai lauyoyin sa.

Babban Lauya na Gidi, Wole Olanipekun, wanda shi ne jagoran lauyoyin kare Onnoghen su 46, ya tashi ya fara kalubalantar haramcin gurfanar da Onnaghen a Kotun CCT.

Wole ya rika kawo ayoyi birjik daga cikin kundin dokokin Najeiriya, masu nuna cewa Kotun CCT ba da ta ‘yancin sauraron karar, don haka haka bai kamata a gurfanar da wanda suke karewa a kotun ba.

“Ina so kafin a fara komai, sai Mai Shari’a ya fara tabbatar mana da hujjojin cewa ya na da ikon sauraren wannan karar tukunna”. Inji Olanopekun.

Ya ce tunda ba a taba kama Onnoghen da wani lafi ba, a bangaren Hukumar Shari’a ta Kasa, haramun ne kotun CCT ta saurari shari’ar sa kai tsaye.

Olanipekun ya kara da cewa sannan kuma ta ya za a gurfanar da mutum kotu alhali ba a ba shi isassshen lokacin da zai shirya kare kan sa a gaban mai shari’a ba?

Lauyan Gawamnati Aliyu Umar ya ce shi ma ba a dade da ba shi bayanan shigar da karar ba. Amma kuma sai wanda ake kara ya kawo kan sa a gaban kotu, sannan ne zai iya kalubalantar cewa bai kamata a gurfanar da shi a kotun ba tukunna.

Aliyu Umar: “Sai wanda ake kara ya fara zuwa kotun tukunna, daga nan idan ya na da korafi, sai ya ce bai yarda a gurfanar da shi a kotun ba.”

Olanipekun: “Haba aboki na abin nan fa ka sani, ni ma na sani. Amma ka na kawo bayanin abin da ka ke tunani. A na magana ce fa a kan abin da doka ta ce, ba tunanin wani ba.”

Olanipekun ya ci gaba da karanto hujjoji daga wata shari’a da aka taba yankewa ya na kafa hujja cewa ba fa zai yarda a gurfanar da wanda ake zargi ba, domin ba a bi ta ka’idojin da suka kamata a gurfanar da shi ba.

Bayyanar wanda ake kara ba ta zama tilas ba, har sai an zo kan batun gurfanar da shi”. Inji Olanipekun.

Aliyu Umar ya ci gaba da cewa bai kamata kotu ta saurari batun lauya Olanipekun ba, sai an gabatar da wanda ake kara tukunna.

Karshe dai Aliyu ya amince cewa ya bada lokaci a sake aika wa Onnaghen da wani sabon sammacen daban, kuma a cikin wannan satin.

Olanipekun ya ce bai yiwuwa a sake komawa kan batun wannan shari’a a cikin wannan makon, domin abin ya shafi sake aikawa da wani sammaci ga Shugaban Alkalai kai tsaye.

Mai Shari’a ya amince da batun Olanipekun, inda ya dage sauraren karar yiwuwa korashin yiwuwar sauraren karar zuwa Talata ta sama.

Share.

game da Author