Tinubu ne wuka shine nama a Kamfen din tazarce dina – Inji Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC Bola Tinubu ne wuka shine kuma nama a kamfen din sa da za a dulmiya ciki gadan-gadan.

Buhari ya fadi haka ne da ya ke kaddamar da kwamitin kamfen din sa a dakin taro na ICC dake Abuja.

Buhari ya ce duk da cewa tare da shi za a zazzagaya ko ina a fadin kasar nan domin tallata kansa a karo ta biyu Tinubu ne zai jagoranci wannan tafiya 100 bisa 100.

” Saboda haka kowa ya ke bukatar wani abu, ya garzaya kai tsaye wajen Tinubu, yananan a kowani lokaci domin sauraran ku. Kuma ina tabbatar muku cewa a wannan kamfen mu maida hankali akai ba zai sa a samu matsala a harkar ci gaba da gudanar da mulki yadda ya kamata ba.

Kowa ya san abinda zai yi a wannan tafiya sannan da irin rawar da zai taka domin mu kai ga samun nasara a wannan abu da muka sa a gaba.

Buhari ya kara da cewa manyan abubuwan da zasu tallata wa mutanen Najeriya shine irin nasarorin da gwamnatin sa ta samu a tsawon shekaru uku da suka gabata. Ya ce gwamnatin sa ta yi kokarin dawo wa Najeriya da martabar ta a idanuwar mutanen Duniya sannan ta yi kokarin ganin ta samar wa mutanen kasar ababen more rayuwa bayan irin ta’asar da gwamnatin PDP ta tafka a tsawon mulkin ta na shekaru 16 a kasarnan.

Bayannan Buhari ya yi alkawarin ganin cewa an gudanar da zabuka masu zuwa cikin kwanciyar hankali da tsaro da kuma gaskiya.

Share.

game da Author