THIERRY HENRY: Monaco ta kore shi bayan shafe kwana 104 ya kasa gudu ya na tsalle wuri daya

0

Maganar gaskiya dama can su dai ‘yan wasan Monaco ta Faransa ba su so kulob din ya kori wancan mai horas da su ba, mai suna Leonardo Jardim.

Rashin tabukawar da Jardim ya i kafin a kore shi, bai hana ‘yan wasan kaunar sa ba, domin su na ganin ya kamo hanyar kokartawa kulob din ya rika samun nasara, sai aka kore shi aka maye gurbin sa da Thierry Henry.

Henry tsohon dan wasan kasar Faransa ne, kuma ana matukar girmama shi a kasar. Wannan girma da aka bai wa Henry, ya dan rika kumbura masa kai, har ta kai shi ga nunawa a fili cewa shi fa ladabi da biyayya ya ke bukata ga yaro.

Maimakon Henry ya dauki salo irin na tsohon abokin wasan sa, Zinedine Zidane a lokacin da ya ke koyarwa a Madrid, inda ya maida kowane dan wasa abokin sa, ciki kuwa har da dan cikin sa, sai Henry ya dauki girman kai ya dora a kan sa a lokacin da ya mike kafa a Monaco a matsayin san a mai koyarwa.

Ya yi rashin sa’a daga farkon shigar sa, ya shiga da kafar hagu, domin bai fara tabuka komai ba, har ma ta kasance wasu na ganin gara ma mai koyarwar da aka kora aka dauko Henry din.

A na su bangaren, ‘yan wasa ba su jin dadin koyarwar Henry, saboda yadda ya ke tsare-gida da kumbura-fuska, maimakon ya rika sakar musu jikin sa.

A ranar 11 Ga Disamba, Henry ya shawo kwana da fadi, a inda tozarta mai tsaron gidan Monaco, Loic Badiashile, bayan an tashi daga taron manema labarai a ranar da Monaco ta yi wasa da Brussia Dortmund.

Shi ma Badiashile ana ganin kimar sa a Faransa, domin ya shafe shekaru 20 ya na tsaron raga.

Wulakanta tsohon dan wasan da ya yi a bainar jama’a, don kawai bai tura kujerar sa a karkashin teburi bayan tashi daga taron manema labarai, ya bata wa kowa rai banda ma shi kan sa wanda aka tozarta din.

Tun daga ranar su ma ‘yan wasa sai suka murje idon su, su ka daina ganin girman sa kuma suka daina yi masa biyayya ko irin ladabin da ya fi so a yi masa.

Henry dan shekaru 41, ya na da dabi’un da har yau za a iya cewa kamar bai girma ba, domin ganin kan sa ya ke yi kamar har yanzu shi dan wasa ne, ba mai koyar da wasa ba.

A cikin kwanaki 104 da ya shafe a Monaco, har zuwa ranar da aka kore shi, a wuri daya ya ke ta daka tsalle, ya kasa gudu.

Ya masu Monaco ta na matsayi na 19 a teburin League 1 a lokacin da aka kori wancan mai horaswa.

Henry ya yi wasan League 1 har guda 12, amma kuma har ila yau dai a matsayi na 19 kungiyar ta Monaco ta ke.

Monaco ta maido da tsohon mai horas da ‘yan wasan da suka kora Leonardo Jardim.

Share.

game da Author