Taron Buhari ya gigita PDP a Kaduna

0

Jam’iyyar PDP da magoya bayan ta sun shiga cikin matsanancin rudani a jihar Kaduna ranar Juma’a ganin irin miliyoyin mutanen da suka yi tururuwa a garin domin yi wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari Lale marhaba da zuwa garin Kaduna.

Babu masaka tsinke a ko ina a cikin garin Kaduna tun daga safiyar Juma’a har kusan misalin karfe 7 na yamma da aka kammala taron.

Sai da shugaba Buhari yayi kusan awa 3 daga filin jirgin Kaduna zuwa filin wasa na Ahmadu Bello a dalilin cinkoson mutanen da ke kokarin daga masa hannu da yi masa lale-lale barka da zuwa.

Wannan taro dai ya nuna cewa jam’iyyar APC da Buhari na nan daram-dam da karfin su a jihar Kaduna sannan kuma ya sa da yawa daga cikin ‘yan Jam’iyyar PDP fadawa cikin dimuwa da tsoro ganin irin wadannan mutane da suka halarci filin taron.

A wajen taron gwamnan jihar Kaduna ya tabbatar wa shugaban Kasa cewa a wannan karon, sai ya samu kuri’u fiye da wanda ya samu a zaben 2015 a jihar.

Daga nan sai ya roki jama’a da su yi wa Buhari ruwan Kuri’u a madadin kyautar ranar zagayowar haihuwar sa da zai kasance ranar 16 ga watan Faburairu ne da yayi dadidai da ranar zaben shugaban kasa.

Ana shi jawabin, shugaban Muhammadu Buhari,ya tabbatar wa mutanen jihar cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da yi wa talakawa aiki babu kakkautawa.

Darektan Kamfen din Buhari, Rotimi Amaechi, ya roki mutane ne da su tabbata sun kare kuri’un su yana mai cewa jam’iyyar PDP na shirin yin magudi a zabukka ma su zuwa.

Daga nan ne fa bayan kammala jawabai da manyan baki suka yi sai shugaban Buhari ya daga hannun gwamnan Nasir sama yana mai kira ga mutanen jihar da su tabbata sun zabe shi domin ci gaba da kwankwadar romon dimokradiya da yake ta kwararo wa mutanen jihar Kaduna.

Shi kuma gwamna Nasir, bayan godiya sai ya nuna mataimakiyar sa, Hadiza Balarabe ga mutane sannan ya yi kira ga mata a jihar da su fito kwan su da kwarkwata su zabe jam’iyyar APC tun daga sama har Kasa.

Share.

game da Author