TARIN FUKA: Najeriya ta samu tallafin naira Tiriliyan 2.6

0

Asusun tallafawa wa kasashen duniya ta tallafa wa fannin kiwon lafiyar Najeriya da Naira tiriyan 2.6 domin dalike yaduwar cutar tarin fuka a kasar.

A takarda da ya fito daga ma’aikatar kiwon lafiya jami’in ma’aikatar Boade Akinola ya sanar wa PREMIUM TIMES da wannan kwazo.

Akinola ya ce asusun za ta biya ma’aikatar kiwon lafiyar kasar nan wadannan kudade ne daga yanzu har zuwa 2020.

Karamin Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa dole ne a hada hannu domin ganin an kawar da tarin fuka a kasar nan ganin cewa bincike ya nuna cewa cutar na cikin jerin cututtuka tara dake yin ajalin mutanen kasar.

” A dalilin yaduwar cutar yara da dama sun zama marayu a kasar nan da hakan ya zama mana dole mu maida hankali wajen ganin an kau da cutar.

Ehanire ya kara da cewa bayan tallafin da ake samu mutane sama da miliyan daya dake dauke da cutar na samun kula ta musamman daga gwamnati.

Ya kuma ce gwamnati ba za ta yi kasa-kasa ba wajen daukan matakan da za su taimaka mata wajen ganin ta kawar da cutar a kasar nan..

” Gwamnati a shirye take domin ganin ta hada hannu da sauran sassan gwamnati, hukumomi masu zaman kansu da kungiyoyin bada tallafi don ganin ta cimma wannan buri nata.

A karshe jami’in asusun Mark Edington ya jinjina kokarin da gwamnati tarayya ta yi wajen ganin ta ware kashi daya daga cikin kasafin kudinta domin inganta fannin kiwon lafiya.

Share.

game da Author