TARIN FUKA: Najeriya ta sami tallafin Dala Miliyan 29

0

A yau Laraba ne jami’in hukumar gudanar da bincike kan cututtuka ta Najeriya (IHVN) Patrick Dakum ya bayyana cewa asusun tallafa wa kasashen duniya za ta tallafa wa Najeriya da dala miliyan 29 wajen dalike yaduwar cutar Tarin Fuka.

Dakum ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja ranar Laraba.

Dakum ya ce bincike ya nuna cewa a Najeriya duk awa daya mutane 47 na kamuwa da tarin fuka da akalla mutane bakwai daga cikin su yara kanana ne. Sannan kuma a duk awa daya mutane 18 wanda ya hada da yara da mata na mutuwa a dalilin kamuwa da cutar a kasar nan.

Bayan haka an samu tabbaci akalla kashi 27 bisa 100 daga cikin mutanen dake dauke da cutar ne ke samun kula a kasar nan.

A dalilin haka Dakum yace za a yi amfani da wadannan kudaden ne wajen inganta kula ga masu fama da cutar ta hanyar hada hannu da asibitoci masu zaman kan su domin ganin hakan ya faru.

” Daga yanzu za mu rika biyan wani kaso daga cikin kudaden da asibitoci masu zaman kan su ke karba daga hannun masu dauke da cutar a asibitocin su. Hakan zai taimaka wajen gaggauta gano cutar da kuma dakile yaduwar ta.

Share.

game da Author