TAMBAYA: Me shari’ah yace game da aikin mace mai aure da yin mua’mula da maza a wurin aiki? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Me shari’ah yace game da aikin mace mai aure da yin mua’mula da maza a wurin aiki?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW

Hakika shari’ah ta hana cuddanyar maza da mata ako ina. Kuma abinda yake faruwa a ma’aikatu na bararrakewa tsakanin mata da maza bai
halatta ba a musulunce. Hira, kebewa, kadaituwa, raha, zolaya, annashawa da sauran su, tsakanin mata da maza yana haifar da barna mai
yawa, yana gusar da kunyar ‘ya mace, yana gusar da kwarjinin da namiji, shedan yana samon damar haifar da fasadi tsakanin maza da mata
da sauran illoli da baza su kirgu ba.

Musulunci bai hana mata fita domin aiki ba, hasilima an yi umurni ga duk musulma ta nemi arziki daga falalan Ubangiji SWT. Saidai hakan
baya nufin mata su cakudu da maza, ko su shiga cikin hadari, ko kuma su jefa maza cikin fitina.

Mata su nada hakkin yin aiki da neman arziki a shari’ance, amma wajibi ne a samar musu da yanayi mai walwala da tsari mai kyau ta hanyar da babu cudanya da maza. Idan hakan bai samu ba, to lallai ne ayi taka tsantsan a wajen aiki da kuma bin ka’idojin musulunce wajen mu’amalar aiki. Mata su sanya suturar kamala, su kare mutuncinsu, su kama maza su runtse idanunsu, kuma su karrama matan. A kaucewa kadaita tsakanin
namiji da mace, abi ka’idojin aiki, kuma ayi aikin batare da kwarkwasa ba. ko rangwada, da sauran kissa irin ta mata. Ayi komai kai tsaye
kawai. A kame daga hira da tsawon zama tare da sakin fuska mara kangado.

Wajibin ma’aikatan ne (maza da mata) su kiyaye dukkan dokokin Allah yayin aiki da wajensa, domin kaucewa tarkon shedan. Duk wanda yafada
cikin tarkon shedan, to fa ba shida wani uzuri a wajen Allah. Lalle ne shugabannin ma’aikata su sanya ido domin kaucewa halaka. Idan aka
sabawa Allah, to Allah zai yi fushi da kowa a wannan ma’aikata kuma hakan zai iya jawo tababarewan wannan ma’aikata harma da ma’aikatan.

Hadisi ya inganta Annabin Tsira SAW yancewa: ido yana zina, kuma zinarido ita ce kallo. Baki yana zina, kuma zinar baki ita ce magana.
Kunni yana zina, kuma zinar kunni ita ce saurare, Kafa tana zina, kuma zinar kafa ita ce tattaki. Hannu yana zina zinar hannu ita ce tabawa. Farji shi ne mai tabbar da zinar. Wannan yana hukunta cewa ma’aikata (maza da mata) su tsare dukkan gabobinsu a cikin aiki da wajen aiki. Allah ya bamu ikon tsarewa. Kuma ya taimaki duk ma’aikatanmu. Amin.

Allah ya tsare mana imaninmu da mutuncinmu Amin.

Share.

game da Author