TAMBAYA: A wane lokaci ne uba ke cire hannun sa a al’amuran ‘ya’yan sa?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
A shari’ance mahaifi yanada daman cire hannun sa akan dawainiyar ‘ya’yan sa maza daga sun balaga mata kuma daga ya aurar da su kuma
suntare a gidajen su. Amma mahaifi yanada wannan damar ne idan ya kyautata tarbiyyar ‘ya’yan sa ta hanyar da za su tsayu da kafafunsu.
Da zarar ‘ya’ya maza sun balaga kuma suna iya tsayuwa da kan su, to dawainiyar rayuwar su tana kan su, shi kuma mahaifi wajibin sa ne ya
dorasu kan turbar da za su tsayu da kan su kafin su balaga. Indan mahaifi ya kasa, to yanada kyau ya ci gaba da kula da su har su kai
munzalin da za su tsayu da kafansu.
‘Ya’ya mata kuwa ‘yan gata ne a Musulunci, dawainiyar su ba ta hawa kansu, ko dai tana kan iyaye, ko mazajen auren su ko kuma kan wasu ‘yan-uwan su na kusa.
A wani bagaren kuma iyaye za su ci gaba da sa ido a kan ‘ya’yan su, da bibiyan lamarin su, a wani bangaren kuma iyaye ba su da damar cire hannayen su akan ‘ya’ya.
Wajibin iyaye ne su ci gaba da yima ‘ya’yansu addu’ah, nasiha, wa’azi, shawara da sa su akan duk wata hanyan alhairi, da kawar da su daga duk wata hanyar sharri. Iyaye su umurci ‘ya’yan su da kyakkawan aiki kuma su hanesu daga mummunan aiki.
Bugu da kari kuma su kyautatawa ‘ya’yansu.
Allah shi ne mafi sani.
Discussion about this post