Kotun Daukaka Kara a Abuja, ta tsige dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP, Jerry Gana, ta maida na farko, wato Donald Duke.
Tun da farko dai Duke din ne ya ci zabe da kuri’a 812, shi kuma Gana ya samu kuri’a 611.
A ranar 4 Ga Disamba, 2018 ne Mai Shari’a Hussein Baba-Yusuf ya cire Duke ya maye shi da Gana, wanda ya kai kara ya ce bai yarda da tsaida Duke ba.
Baba-Yusuf ya kafa hujja da cewa ka’idar jam’iyyar SDP ta nuna cewa dan takarar shugaban kasa ba zai fito daga shiyya daya da shugaban jam’iyya ba.
Wannan ne ya sa Baba-Yusuf ya ce wa SDP da INEC Gana ne halastaccen dan takara.
Su kuma shugabannin jam’iyya suka garzaya Kotun Daukaka Kara, domin rashin amincewa da hukuncin Babbar Kotun Tarayya.
A yau Alhamis an maida wa Duke halascin takarar sa, aka tsige Gana.
Sai dai bayan wannan shari’a da kotu ta yanke jiga-jigan jam’iyyar sun ce za su yi zama na musamman domin yanke shawara kan wannan hukunci da kotu ta yanke.
Discussion about this post