SUNAYE: Sabbin DIGs da Sufeto Mohammed ya nada

0

A yau litinin ne Sufeto Janar din ‘Yan sandan Najeriya ya nada sabbin DIGs, wato mataimakan Sufeto Janar 7.

Hakan ya biyo bayan yi wa wasu 7 murabus da aka yi a makon jiya.

A cikin wadanda aka nada akwai tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibarahim Lamurde daga jihar Adamawa.

Sauran sune, Usman Tilli Abubakar, daga jihar Kebbi, Taiwo Frederick Lakanu, daga jihar Legas, Godwin Nwobodo, daga jiha Enugu,
da Ogbizi Michael daga jihar Abia State.

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya yi wa Manyan Mataimakan Sufeto Janar su bakawi ritaya daga aiki.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa wadanda sallamar ta shafa sun hada Maigari Dikko, Habila Joshak, Agboola Oshodi-Glover, Mohammed Katsina, Sani Mohammed da kuma Peace Ibekwe-Abdallah.

An rubuta musu takardar sallama daga aiki a jiya Lahadi, kuma za a yi sanarwar ce a yau Litinin.

PREMIUM TIMES ta tuntubi sabon Kakakin Yada Labarai na ‘Yan sanda, Frank Mba, amma wayar sa a rufe.

Wadanda aka sallama din dai duk su na gaba da sabon Sufeto Janar wajen mukami, kuma sun riga shi shiga aikin dan sanda.

Ko lokacin da Buhari ya nada Ibrahim Idris cikin 2016, sai da aka yi wa manyan sa 22 ritaya, domin duk su na gaba da shi.

Da dama jama’a na korafi da wannan tsarin na yadda Buhari ke dauko jami’i na kasa da wasu manya da dama ya ba shi mukamin Sufeto Janar.

Share.

game da Author