Sojoji sun saki editan Daily Trust

0

Babban Editan Jaridar Daily Trust Mannir Dan-Ali ya bayyana cewa sojoji da ke rike da editan jaridar na ofishin ta dake Maiduguri jihar Barno Uthman Abubakar sun sake shi.

Sojoji sun yi awan gaba da edita Uthman Abukar ne a lokacin da suka kawo wa ofishin samame a Maiduguri.

Abubakar ya bayyana cewa akwai wayar sa da komfutar sa da ke hannun rundunar sojin cewa basu gama bincike akai ba.
Amma kuma basu muzguna masa ba ko kuma ci masa mutunci.

Idan ba a manta ba Sojoji cike makil a motoci har 5 sun far wa ofisoshin jaridar Daily Trust dake Abuja da na Maiduguri, jihar Barno inda suka rufe ofisoshin sannan suka waske da komfutoci na aiki da wasu ma’aikata a ranar Lahadin da ya gabata.

Babban dalilin da ya sa sojojin suka kai farmaki wadannan ofisoshi kuwa shi ne wai don labaran da jaridar ke wallafa game da ayyukan sojojin a jihar Barno da yadda Boko Haram ke ta samun galaba a kan dakarun kasar nan.

Sannan kuma jaridar ta wallafa shirin da rundunar sojin Najeriya ta yi da dubban sojoji da makaman yaki domin tunkarar garin Baga da wasu garuruwa har guda 5 da ke yanzu a hannun Boko Haram suke.

Share.

game da Author