Sojoji sun kai farmaki ofisoshin Daily Trust da ke Abuja da Maiduguri, sun yi awon gaba da wasu ma’aikata

0

Sojoji cike makil a motoci har 5 sun far wa ofisoshin jaridar Daily Trust dake Abuja da na Maiduguri, jihar Barno inda suka rufe ofisoshin sannan suka waske da komfutoci na aiki da wasu ma’aikata.

Babban dalilin da ya sa sojojin suka kai farmaki wadannan ofisoshi kuwa shi ne wai don labaran da jaridar ke wallafa game da ayyukan sojojin a jihar Barno da yadda Boko Haram ke ta samun galaba a kan dakarun kasar nan.

Sannan kuma jaridar ta wallafa shirin da rundunar sojin Najeriya ta yi da dubban sojoji da makaman yaki domin tunkarar garin Baga da wasu garuruwa har guda 5 da ke yanzu a hannun Boko Haram suke.

Bangaren Boko Haram da ke da alaka da kungiyar ISIS ne suka kwace wannan gari na Baga. Bayannan garuruwa da suka hada da Doron-Baga, Kross Kawwa, Bunduran, Kekeno da Kukawa duk suna karkashin ikon Boko Haram ne kamar yadda Daily Trust din ta rika ruwaitowa daki-daki.

Wasu da abin ya faru a idanuwar su sun bayyana cewa wadannan sojoji sun far wa ofishin jaridar dake Abuja inda suka ce a mika musu wasu ma’aikatan jaridar su uku.

Wani Hamza Idris, Usman Abubakar da Ibrahim Sawab. Sun tafi da Usman Abubakar da Ibrahim Sawab.

Babban Editan jaridan Mannir Dan Ali ya bayyana cewa tuni har sun fara bibiyar abin don ganin an warware matsalar da aka samu.

Wannan abu da ya faru da jaridar Daily Trust da wasu jaridun kasar nan na daga cikin koke-koken da masu aikin jarida ke yi game da wannan gwamnati mai ci.

Share.

game da Author