Shekara uku a mulkin Buhari mutanen Najeriya na dandana kudar su da talauci, Inji Amaechi

0

Ministan Sufuri kuma darektan Kamfen din Buhari 2019 ya koka kan yadda mutanen Najeriya ke fama da matsanancin yunwa da talauci.

A wani faifai da aka dauka bai sani ba, an ji Amaechi yana cewa ” Lallai ana fama da talauci a wannan kasar, babu mai jin dadi kwatata, ba Manoma ba, ‘yan siyasar ma ba dadi suke ji ba sannan su kansu dalibai kuka suke. Kowa na kuka saboda rashin samun walwala yadda ya kamata.

A cikin wannan faifai an ji Amaechi na cewa ” Shi fa Buhari ba ya daukar shawarar kowa abinda yake so ya ke yi, sannan babu abin da ya sha masa kai. Za ka iya rubuta duk abinda kake so abinka bai damu ba, domin ba karatu yake yi ba ma.Idan ma yaga ana sukar sa sai ya kira ka yace zo, zo ka gani wai zagi na suke yi, sai ya fashe da dariya abin sa.

” Akwai wani lokaci da muna tare a jirgin sama sai ya karanta labarin wani mai saida raguna a lokacin Sallah yana korafin rashin ciniki, cewa a gwamnatin Buhari babu kasuwa, sai Buhari ya kira ni ya ce in zo in gani, ko me ya hada shi da rashin saida ragunan sa a Onitcha da shi oho.

” Najeriya ba zata taba canja wa ba na rantse maka, idan ba kowa aka kashe ba kasarnan zata ci gaba da zama wuri daya ne cak.

Phrank Shuaibu, na kamfen din Atiku ne ya fidda wannan faifai da minista Amaechi ya zazzaro wadannan zantuka.

Phrank ya kara da cewa hakan ya dada tabbatar da irin kalaman da maidakin shugaban Kasa, Aisha Buhari ta rika cewa maigidanta ba shine ke gudanar da mulkin Najeriya ba, cewa wasu mutane ne da basu wuce uku ba suke yadda suka ga dama a kasar nan.

Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta nemi ji daga bakin Amaechi, kakakin sa David Iyofor ya ce suna nan suna ci gaba da bincikar wannan faifai domin samun tabbacin abubuwan da aka ce ministan ya fadi.

Share.

game da Author