Shawara, Bakon Dauro, Kwalara da Zazzabin Lasa ‘yan Najeriya suka yi fama da a 2018

0

Shawara, Bakon Dauro, Kwalara da Zazzabin Lasa ‘yan Najeriya suka yi fama da a 2018.

Hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) ce ta bayyana haka a wani rahoto da ta fitar.

Rahoton ya bayyana cewa a 2018 adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar zazzabin lasa ya kai 559 inda daga ciki mutane 143 suka rasu.

NCDC ta bayyana cewa haka ya faru ne a jihohi 22 a tsakain wanin Janairu zuwa Nuwamba.

Rahotan ya nuna cewa jihohin Edo, Ondo da Ebonyi na jikin jihohin da mutane suka fi rasa rayukan su a dalilin kamuwa da zazzabin lasa.

Bayan haka NCDC ta bayyana cewa a 2018 kuma cututtuka kamar su shawara, bakon dauro da kwalara na daga cikin cututtukan da mutane suka yi fama da.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne jami’ar kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Charity Warigon ta bayyana cewa kungiyar WHO za ta ba Najeriya gudunmawar maganin allurar rigakafi zazzabin shawara har na miliyan 12 a shekarar 2018 sannan ta kara bada magani na miliyan 19 a 2019.

Charity ta bayyana haka ne a Abuja inda ta kara da cewa WHO za ta samar da wannan gudunmawa ne da hadin guiwar Kamfanin GAVI.

A wani rahoton hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) zazzabin shawara ta bullo a kananan hukumomi 22 a kasar nan, sannan mutane 4200 sun kamu kuma 47 sun rasu cikin su.

Charity ta ce suna kokarin ganin an kau da wannan zazzabi zuwa 2026.

Share.

game da Author