Dakatar da Cif Jojin Najeriya, Walter Onnoghen da Shugaba Muhammasu Buhari ya yi a jiya Juma’a ya bar baya da kura.
Tun jiya kasar nan ta rude, kuma ra’ayoyin jama’a sun rabu gida biyu. Inda na wadanda ke cewa ba a bi ka’idar dakatar da shi ba, suka rinjayi masu cewa an yi daidai.
WANE NE BABBAN MAI SHARI’A
Shi ne shugaban alkalan Najeriya gaba daya, kuma shi ne shugaban bangaren mulki na cikon uku. Wato Buhari a bangaren zartaswa, Bukola Saraki a bangaren majalisa sai kuma babban mai shari’a a bangaren shari’a.
Kowane daga cikin su zaman kan say a ke yi, doka ba ta yarda wani ya shiga sha’anin wani ba.
IKON NADAWA DA TSIGE CIF JOJI
Shugaban kasa ne ke da karfin nada Babban Mai Shari’a, amma kuma ba shi kadai ke da karfin ikon cire shi ba.
Kundin tsarin mulkin Najeriya a Sashe na 292, ya ce shugaban kasa zai iya raba Cif Joji da mukamin sa idan ya aika da bukatar yin haka ga Majalisar Dattawa. Sannan Cif Joji ba zai taba tsiguwa ba daga kan kujerar sa sai har kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisa sun amince da a tsige shi.
Wannan dalili ne jama’a da dama ke cewa Buhari ya yi barambarama da ya dakatar da Cif Joji ba tare da neman izni daga majalisa ba.
ASHE BA CIF JOJI KADAI BA NE
Akwai sauran manyan mukamai na manyan masu shari’a da doka ba ta amince da shugaban kasa haka kawai ya bugi kirji ya ce ya cire su ba, sai sai da amincewar majalisar dattawa.
Shugaban Kotun Daukaka Kara na cikin su, haka Shugaban Babbar Kotun Tarayya da na Babbar Kotun Najeriya da Babbar Kotun FCT da Alkalin Alkali na Kotun Shari’ar Musulunci da Shugaban Kotun Shari’ar Gargajiya. Akwai kuma Shugaban Kotun Daukaka Kara ta FCT.
Dukkan wadannan doka ba ta yarda shugaban kasa ya cire su ba tare da amincewar kashi biyu bisa uku na Majalisar Dattwa ba.
DA WADANNE DALILAI ZA A IYA CIRE SU?
Kundin Dokar Najeriya a cikin sashe na 292 ya ce sai idan wanda za a cire din ya nuna kasawa wajen gudanar da aikin sa.
WACE IRIN KASAWA CE?
Idan ya kasa yin amfani da kwakwalwar sa ko tunanin sa ko hankalin sa wajen gudanar da aikin sa.
Ko kuma wata tawaya ko nakasa a bangare ko sashen jikin sa ta hana shi iya gudanar da aikin sa.
Ko kuma idan ya karya dokar ka’idojin gudanar da aikin shari’a da Kotun CCT ta shimfida.
SHIN BUHARI YA BI WADANNAN KA’IDOJI?
Buhari ya dakatar Cif Jojin Najeriya a ranar Juma’a, kwana daya bayan da Kotun CCT ta bas hi odar ya dakatar da shi, domin kotun ta ci gaba da tuhumar sa zargin kin bayyana kadarorin sa da ta ke yi masa.
Buhari bai jira ya kai batun a gaban Majalisar Dokoki ba, ballantana har a yi mahawarar amincewa ko rashin amincewa, har kuma a samu kashi biyu bisa uku na masu goyon bayan a dakatar da shi.
KO KOTUN CCT TA IYA TUHUMAR CIF JOJI KAI-TSAYE
Kotun CCT ba za ta iya tuhumar Cif Jojin Najeriya kai-tsaye ba, har sai Majalisar Shari’a ta Kasa, wato NJC ta bincike shi ta tabbatar da akwai zarge-zargen da ake yi masa sun tabbata. Sannan ne za ta bada umarnin a gurfanar da shi a gaban kotun CCT.
Ba a yi wa Walter Onnoghen haka tun da farko ba, sai aka tura karar sa kai tsaye ga CCT. Dalili kenan shi kuma ya ki halarta har zama na biyu, inda shi da lauyoyin sa duk suka ce ba a bi kan ka’idar gabatar da shi kotu ba. Don haka ba zai yarda gwamnatin tarayya ta gurfanar da shi ba.
Discussion about this post