SHARI’AR DASUKI: Kotu ta ci gaba da sauraren kara ba tare da bayyanar Dasuki ba

0

A ci gaba da shari’ar tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Tsaro, Sambo Dasuki, a jiya Laraba Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama Abuja, ta ci gaba da shari’a ba tare da bayyanar wanda ake kara a kotun ba.

Ana tuhumar Dasuki ne tare da Bashir Yuguda, Dalhatu Investiment Limited, Sagir Attahiru da kuma Attahiru Bafarawa a bisa zargin karkatar da kudade kimanin naira bilyan 19.4.

Dasuki ya na tsare tun cikin 2015, duk da cewa kotu ta bayar da umarnin a sake shi a bisa beli.

Cikin 2018 ne Dasuki ya ce ba zai sake zuwa kotu ba, tunda ita ma gwamnatin tarayya ta bijire wa umarnin kotu, ta ki sakin sa a kan beli.

A jiya Laraba, lauyan EFCC Oluwaleke Atolagbe, ya shaida wa kotu cewa mai gabatar da shaida ya na kotun, kuma a shirye ya ke ya bayar da shaidar hujjoji.

Amma Atolagbe ya ce ba za a iya ci gaba da, tunda Dasuki bai yarda an kawo shi kotun ba.

Shi kuma lauyan Dasuki mai suna Victor Okudili, ya nemi kotu a dage shari’ar har sai yadda hali ya yi, kuma sai EFCC ta bi umarnin Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu, wadda ta bayar da belin Dasuki tun a ranar 2 Ga Yuli, 2018.

Mai Shari’a Hussain Baba-Ahmed ya dage sauraren sai ranar 19 Ga Fabrairu domin ya san abin da zai zartas.

Share.

game da Author