SAURIN MANTUWA: Ana ci gaba da nuna damuwa kan rashin kuzarin Buhari

0

A jiya Alhamis ne Shugaba Muhammadu Buhari ya buga shirme da abin kunya a dandalin kamfen, a garin Warri, babbban birnin Jihar Delta.

Ya yi abin kunyar ne a lokacin da zai mika tuta ga dan takara na gwamnan jihar, a karkashin jam’iyyar APC, wato Great Ogboru.

Yadda abin ya faru kuwa shi ne: A yayin da shugaban jam’iyya na kasa, Adams Oshiomhole ya je ya mika wa Buhari Tuta, shi kuma ya mika wa Ogboru, maimakon ya ce ya mika tuta ga dan takarar gwamna, sai ya tabka kuskure kamar haka:

“Ina mai mika wannan tuta ga dan takarar shugaban kasa”. Inji Buhari a cikin mantuwa da sakin layi.

Nan da nan sai manyan bakin da ke kewaye da shi, suka yi sauri su ka gyara masa, suka ce, “Dan takarar gwamna dai.”

Maimakon ya ce, “ga dan takarar gwamna, sai ya sake yin-subul-da-baka, ya ce “ga dan takarar sanata.”

Wadanda ke kewaye da shi kuma suka sake cin sa gyara a cikin hanzari, suka ce, “dan takarar gwamna.”

Sai a wannan karo na uku ne ya ambata daidai, ya ce “dan takarar gwamna.”

ANA WATA GA WATA

Bayan Buhari ya damka masa tuta, ya kuma ba shi hannu suka gaisa. A nan ma saida Buhari ya sake kwafsawa, ya ce: “Madam ina yi miki fatan alheri.” Haka Buhari ya waiwaya ya furta wa wata mata wadda matar Ogboru din ce.

Nan da nan kuwa masu adawa da kuma dimbin ‘yan Najeriya suka yi amfani da wannan damar suka yi wa Buhari caa, inda kowa na bayyana ra’ayin sa cewa akwai matsala tattare da Buhari, don haka bai kamata ya sake shekaru hudu a kan mulki ba.

Don haka wasu na cewa sake hawan sa ganganci ne, wasu kuma na cewa ya tafi Daura ya huta kawai.

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, cewa ya yi: “Shin wai su masu tallar wannan mutumin ba su da kunya ne? Shekaranjiya a NTA ya kwafsa. Yau kuma a Delta ya sake kwafsawa. Shin ba za su bar shi ya tafi gida ya huta hakanan ba ne?”

Share.

game da Author