Dukkan Sanatocin Jam’yyar APC sun tsame kan su daga yunkurin da sanatoci suka yi inda suka bayyana maka Shugaba Muhammadu Buhari kara a Kotun Koli, dangane da dakatar da Cif Jojin Najeriya, Walter Onnoghen da ya yi ba tare da tuntubar Majalisar Dattawa ba.
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ne ya bayyana haka a jiya Litinin, inda ya kara da cewa su dai sanatocin APC ba su taba yin wani zaman da suka tattauna batun maka Buhari Kotun Koli ba.
Tun da farko kakakin shugaban majalisar Dattawa, Yusuf Olaniyonu ne ya bayyana cewa Majalisar Dattawa ta shigar da kara a Kotun Koli, ta na kalubalantar Buhari a kan kasassabar dakatar da Onnoghen ba tare da tuntubar ta ba.
Sai da kuma Sanata Lawan ya ce ya na magana ne a madadin sanagtoci na APC, kuma ya ce a matsayin sa na shugaban masu rinjaye, majalisa ba ta yi wani zaman zartas da hukuncin maka Buhari kara ba.
Don haka ya ce dukkan sanatoci da ke karkashin APC sun kauda kan su daga wannan shiri da ya ce ba a yi da sub a, kuma ba su goyi baya ba.
Amma dai Olaniyonu ya hakikice cewa shugabannin majalisar dattawa sun yi zaman da yanke shawarar maka Buhari kotun.