Hukumar Kula Da Aikin Dan sanda ta Kasa ta ce ta samu takardar neman aikin shiga dan sanda daga matasa sama da 294,000.
Hukumar ta ce an samu wannan adadin, duk kuwa da cewa gaba daya guda 10,000 ne kadai za a dauka.
Ta ce a yau Juma’a ne aka rufe turakar shiga a nemi aikin dan sanda din a shafin intanet.
Hukumar ta yi shirin daukar kuratan ‘yan sanda 10,000 a bisa umarnin Shugaba Muhammadu Buhari na kokarin kara inganta tsaro.
Kakakin Yada Labarai na hukumar, Ikechukwu Ani, shi ya bayyana haka jiya a Abuja, bayan fara karbar fam na masu neman aikin ta cikin intanet tun a ranar 28 Ga Nuwamba, 2018.
Ya ce ‘yan Jihar Neja sun fi yawa har su 17, 790 sai kuma jihar Katsina su 16, 800, Katsina, Bauchi kuma 16, 666, sai Kaduna su 12, 652.
Gaba daya inji shi, an samu maza 255,189 sai kuma mata 39,662 a fadin kasar nan.