Rundunar Sojojin Sama ta ta ce sojojin ta na ‘Operation Idon Mikiya’ sun lalata wani sansanin ‘yan bindiga tare da kashe da dama daga cikin su.
Ibikunle Daramola wanda shi ne Daraktan Yada Labarai, ya ce an karkashe ‘yan bindigar ne kusa da Tsaunin Doumbourou, a Jihar
An kai musu harin ne bayan an samu wasu rahotannin bayanan inda mabuyar mahara din suke a kusa da tsaunin.
Masu leken asiri da na’urori sun tabbatar da hango maharani inda sukan rika taruwa a wani gida da ke kusa da tsaunin kafin su fita kai hare-hare.
Harin farko ya lalata gidan tare da kashe mahara da dama.
A hari na biyu kuma da aka sake kaiwa, an kai shi ne a kan sauran maharan da suka tsere yayin da suke sake taruwa, inda aka sake bude musu wuta aka karkashe su.