Sojojin Birged ta 23 da ke Yola, wadanda aka tura domin dakile rikicin kabilanci tsakanin kabilar Lunguda da Waja na cikin Kananan Hukumomin Guyuk da Lamurde, sun kama mutane 71.
Kwamandan Birged din Birgediya Janar Bello Abdullahi ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke damka wadanda aka kama din a hannun ‘yan sanda domin ci gaba da binciken su.
Ya ce an kara girke sojoji a yankin domin hana sake afkuwar wani sabon rikicin. Ya kara da cewa sun kwato makamai irin su bindigun gargajiya, adduna, kwari da baka da sauran su duk a hannun wadanda ake zargi din.
Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya ruwaito cewa an kona amfanin gona mai tarin yawa yayin rikicin.