Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Fatakwal ta harmta wa jam’iyyar APC shiga zaben 2019 a jihar.
Mai Shari’a Kolawole Omotosho ne ya zartas da wannan hukunci a yau Litinin tare da gargadin INEC cewa kada ma ta bata lokacin shigar da APC a zaben 2019 a jihar Ribas.
Dama bangarorin jam’iyyar APC na jihar sun gudanar da zaben fidda gwani daban-daban.
A daya bangaren akwai na mabiya minista Rotimi Amaechi da kuma daya bangare na mabiya Magnus Abeh
Bangaren Amaechi ya fitar da Tonye Cole a matsayin dan takara, shi kuma daya bangaren ya fitar da Magnus Abe.
Sai dai kuma ita APC ta kasa ta amince da zaben Tonye Cole na bangare Amaechi a matsayin dan takarar ta. Kuma sunan sa ne aka bai wa INEC.
Bangaren Abe ne ya kai kara, inda Mai Shari’a ya yi tir da yadda bangaren Amaechi ya ki bin umarnin kotu, ya yi gaban kan sa wajen gudanar da zaben fidda gwani.
Kotu ta ce duka zabukan fidda gwanin da aka gudanar, an yi su ne a lokacin da aka rigaya aka gabatar da kara, kuma Babbar Kotun Jihar ta haramta a yi zaben sai ta yanke hukunci tukunna.
Don haka ganganci ne da raina kotu da kuma raina dokar kasa ya sa APC ta gudanar da zaben fidda gwani a jihar.
Shi ya sa ya ce hukuncin da Babbar Kotun jiha ta yanke ya nan daram, cewa zaben fidda gwani na jihar Ribas haramtacce ne.
Kotu ta ce INEC da APC duk su yi watsi da sunan dan takarar gwamnan jiha, Tonye Cole da na sauran ‘yan takara da APC bangaren Amaechi suka gabatar musu.
Haka kuma ya ce zaben fidda gwani da bangaren Magnus Abe ya gabatar haramtacce ne, saboda uwar jam’iyyar APC ta kasa ba ta tura wakilai sun shiga zaben ba.
A kan haka mai shari’a ya ce shi ma bangaren Magnus Abe ba zai shiga zaben 2019 a jihar Ribas ba.
Kanan hatta zaben shugaban kasa APC ba za ta shiga ba.