RASUWAR SHAGARI: Buhari ya fadi ba nauyi a gaban mu, bayan rasuwar mahaifin mu – Aminu Shagari

0

Aminu Shagari, wanda da ne ga tsohon Shugaban Najeriya, Shehu Shagari, ya bayyana rashin halascin da ya ce Buhari ya yi musu bayan rasuwar mahaifin na su.

Ya yi wannan fallasa ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da jaridar PUNCH a jiya Lahadi.

Ya ce duk da mahaifin su ya gafarta wa wadanda suka cuce shi, amma bai taba mantawa da cutar da suka yi masa ba. Ya na magana ne a kan yadda Buhari a matsayin sa na babban jami’in soja, ya ci amanar shagari, har ya hambarar da gwamnatin sa cikin 1983.

Shagari wanda ya yi shugabanci daga 1979 zuwa 1983, ya rasu ne a ranar 28 Ga Disamba, 2018, a daidai shakaru 93 a duniya.

Buhari ya je Sokoto a ranar 30 Ga Disamba, domin ya yi ta’aziyyar Shagari ga iyalan sa.

A cikin hirar da PUNCH ta buga a jiya Lahadi, an tambayi Aminu Shagari shin wane darasi ya koya, ganin wanda ya yi wa mahaifin sa juyin mulki, yace bai iya ba, amma ya je ta’aziyya ya na yabon irin mulki da halayya ta mahaifin na su, wato Shagari?

Aminu ya ce maganar gaskiya ba su ji dadin yadda Buhari ya nuna ba a lokacin ta’aziyyar da kuma kafin rasuwar sa.

“Har mahaifin mu ya rasu, wanda ya hambarad da shi bai sake ba shi wani kulawa ko mutuntawa ba, duk kuwa da cewa bayan ya hambarad da shi, ya bincike shi, amma bai kama shi da aifin komai ba.”

“Da farko dai bari na fara da cewa duk da mahaifin mu ya yafe wa wadanda suka ci amanar sa, amma ka san babu yadda za a yi mutum ya manta irin abin da aka yi masa.

“Mu din nan kankin kan ku mun nuna wa Buhari goyon baya. Amma tun daga lokacin da ya zama shugaban kasa, ba zan ce akwai wani batu da ya taba sa ya tuntube mu ba.

“Ai kamata ya yi a ce mutumin da yake makusanci na kwarai ga mahaifin mu har ya yi masa juyin mulki, ya dan saurare su, ko ya dube mu da mutunci.”

Ya kara da cewa ko ta’aziyyar da ya kai dama ba su yi tunanin wasu kalamai na kirki na tausar da zukata za su fito daga bakin Buhari ba.

“Lokacin da ya shigo gidan mu, mun yi tsammanin jin wasu dadadan kalamai daga bakin sa. Amma ba mu ji komai ba, saboda bai ce komai ba din. Mu ka ba shi littafin da wadanda suka je ta’aziyya ke sa hannu, amma sai kawai ya sa hannu kadai, ko sunan sa bai rubuta ba cikakke, sai ya kuma rubuta ranar da ya je.

“Maganar gaskiya raina ya baci matuka da wannan dabi’a ta Buhari. A zato na a matsayin sa na musulmi, ko addu’a sai ya yi, ya ce: Allah ya gafarta masa, mu ma idan ta mu ta zo, Allah ya gafarta mana’. Wannan ne ya sa rai na ya baci matuka da Buhari.” Inji Aminu Shagari.

Share.

game da Author