Shahararriyar Kungiyar Fafutikar Yaki da cin hanci da rashawa mai suna Transparency International, ta ce har yanzu Najeriya tsamo-tsamo ta ke cikin dagwalon kazantar cin hanci da rashawa, kamar dai yadda ake a baya.
Yau Talata ne TI ta fitar da jadawalin lalacewar cin hanci da rashawa da ta kan fitar a duka shekara.
A wannan da ta fitar na shekarar 2018 da ta gabata, TI ta ce maganar gaskiya Najeriya ba ta samu wani cigaba ba, kuma ba ta koma baya ba a batun cin hanci da rashawa.
TI ta ce har yanzu Najeriya a matsayin ta na da ta ke. Wato a na nan dai ‘yar gidan jiya kenan.
Kungiyar CISLAC da TI sun shaida wa PREMIUM TIMES a yau Talata cewa Najeriya ta samu maki 27 kacal daga cikin 100 a 2018. Wato ta rike kambun ta na 2017 kenan a batun lalacewar cin hanci da rashawa.
A wannan lissafi na 2018, Najeriya ta zo ta 144 a jerin kasashen da ke da rangwamen rashawa su 180. Sai dai kuma cikin shekarar 2017, ta zo 148 a cikin kasashen 180.
Jama’a da dama na jiran su saurari gwamnatin Buhari ta yi watsi da wannan rahoton, kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da na 2017.
Buhari ya ce bai amince da sakamakon da TI ta ba Najeriya a 2017 ba, domin ya yi abin a zo a yaba a fannin yaki da cin hanci da rashawa.
Sai dai kuma Mataimakin sa Yemi Osinbajo, cikin watan Fabrairu, 2018, ya ce ya karbi sakamakon da kyakkyawar zuciya, kuma Najeriya za ta kara kokarin yadda a 2018 da ma shekaru masu zuwa za a jinjina mata.
TI ta yi amfani da rahotannin wasu cibiyoyi takwas ne wajen dora Najeriya a sahun bayan kasashen da ake yaki da cin hanci da rashawa a hakikance da kuma a aikace.