Hukumar Ladaftar da Ma’aikata ta jero tulin tuhume-tuhumen da ta ke wa Babban Mai Shari’a na Kasa, Walter Onnogen.
Ta gabatar da tuhumar ce a gaban Kotun Hukunta Ma’aikata a kan Shugaban Alkalan Najeriya, wanda aka nada cikin watan Maris, 2017, kasa da watanni shida bayan an kai farmakin bincike gidajen wasu alkalan kasar nan.
A ranar 10 Ga Janairu, 2019 ne Gwamnatin Najeriya ta shigar da karar da ta kai shugaban bangaren shari’ar Najeriya, inda ta zarge shi da yin karya da kuma saba dokar bayyana kadarorin da ya mallaka.
Tuhumar ta nuna cewa sai cikin 2016 ne bayan gwamnati ta kai samame gidajen alkalai sannan Onnoghen ya bayyana kadarorin sa, amma kuma ya ki ya lissafa har da wasu asusun ajiyar banki da dama wadanda gwamnatin ta ce ya kimshe kudade har da na kasashen waje a cikin su, a Bankin Standard Chartered a reshen sa da ke Abuja.
Dangane da haka ne gwamnati ta lafta masa tuhuma har guda shida, da aka umarci ya gurfana ya bayar da ba’asi a ranar Litinin 14 Ga Janairu, a kotun CCT.
CCT ta bada sanarwar cewa za a fara sauraren karar a ranar Litinin a kotun wadda ke Jabi, Abuja.
Wannan shari’a za ta kara dagula ‘yar tsamar da ke tsakanin bangaren shari’a da kuma bangaren gwamnati, wanda dangantaka ta yi tsami tun bayan farmakin da aka rika kaiwa gidajen wasu masu shari’a, cikin Oktoba, 2016.
Bayan kai wancan samame, an zargi wasu alkalan Kotun Koli su biyu, da laifin cin rashawa, sai dai kuma babu wannan shari’a ta samu ya aikata laifin.
PREMIUM TIMES ta samu dukkan kwafe kwafe-kwafen cajin da ake yi wa Onnoghen, wadanda a bisa kwararan alamu, wata kungiya ce ta kai korafin abin da ya tafka.
Kungiyar dai sunan ta Anti-curruption and Resaerch based Data Initiative, ita ce ta kai kuka a kan harkallar da ta yi zargin Onnoghen ya tabka.
Kungiyar ta aika da kwafen takardun korafin ga ICPC da kuma EFCC.
Sun yi zargin ya kimshe dala 10,000 har sau biyar a ranar 8 Ga Maris, 2011 a bankin Standard Chartered Bank, cikin asusun ajiyar sa mai lamba 1062650.
Ranar 7 Ga Yuni, 2011 kuma, ya kimshe dala 5,000 har sau biyu a rana daya. Sannan a wannan ranar dai ya sake kimshe wata dala 10,000 har sau hudu.
Ranar 27 Ga Yuni, 2011, ya jidi dala 50, 000, zuwa bankin, inda aka rika shigar da dala 10,000 har sau biyar a cikin asusun nasa.
Washegari a ranar 28 Ga Yuni, ya sake kimshe dala 10,000 har sau hudu duk a cikin asusun.
An ce ya saba dokar bayyana kadarori a Shashe na 15(1), na dokar CCT, wadda ta ce ma’aikta su rika bayyana kadarorin da suka mallaka duk bayan shekaru hudu.
Tun 2011 da Onnoghen ya kimshe kudaden, bai bayyana kadarorin sa ba, sai a ranar 14 Ga Disamba, 2016.
Discussion about this post