PDP basu taba cin zaben gwamna a jihar Kaduna ba, murdiya suke yi – Inji El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa a iya binciken da yayi tun bayan hawan sa karagar mulkin jihar Kaduna, ya gano cewa ashe jam’iyyar PDP bata taba cin zaben gwamna ba a jihar.

A tattaunawar da yayi da Talabijin din Channels a safiyar Alhamis, El-Rufai ya bayyana cewa taron PDP da suka yi a garin Kaduna bai dada shi da kasa ba ko kadan hasali ma cewa yayi hayan mutane suka yi.

“ Ai ni taron PDP da suka yi a Kaduna bai dada ni da kasa ba ko kadan domin hayan mutane suka yi, kuma haka suke yi.

Idan ba a manta ba El-Rufai ya fadi irin haka a taron kaddamar da Kamfen din sa inda yace mafiyawan dubban mutanen da suka halarci gangamin PDP a Sokoto daga Nijar aka yo hayan su.

Da aka yi masa tambaya game da zabin musulma da yayi a matsayin mataimakiyar sa, El-Rufai yace yayi haka ne domin ya kau da maganar kabilanci da addini a siyasar jihar. Yace kwarewa da cancantar Dakta Hadiza Balarabe ne babban dalilin da ya sa ya zabe ta amma ba wai don addini ba.

Sannan kuma yace baya tsoron rasa kuri’un da zai yi a yankin kudancin Kaduna wai don yayi haka.

“ Bana fargabar ko zan rasa kuri’u a wannan yanki na Kudancin Kaduna. zan iya ce maka yau koda Paparoma na zaba a matsayin mataimakina, mutanen yankin Kudancin Kaduna sun yanke shawarar ba za su zabe ni ba, ka ga ko menene abin tada hankali a ciki. Mataimakin gwamna na a yanzu kirista ne amma babu wani abu da ya canja. Hasali ma tashin hankali da kiyayya ya jawo masa kawai don suna gani wai shi yana tare da abin da suka kira ‘ Alaka da musulmi ko musulunci.’

“ Duk da ina so in yi nasara a zabe mai zuwa dole in yi taka tysantsan wajen yanke hukunci a kan abinda na sa a gaba.

Share.

game da Author