ONNOGHEN: Majalisar dattawa ta janye dawowa ranar Talata, ta garzaya Kotun Koli

0

Majalisar dattawa ta janye dawowa daga hutu domin yin zama ta musamman don tattauna dakatar da babban mai shari’a Walter Onnoghen da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a makon da ya gabata.

A Maimakon dawowa daga hutun sai kawai majalisar ta buge da garzaya kotun koli domin kotun ta fassara mata dokar da ya bata ikon sai dole an mika a gabanta wannan bukata kafin shugaban kasa ya iya tsige Alkalin Alkalan.

A makon da ya gabata ne Shugaba Buhari ya dakatar da babban mai shari’a Onnoghen bisa laifin kin bayyana kadarorin sa kafin a nada shi Alkalin Alkalai na kasa.

Hakan ya jawo cece kuce matuka inda kowa ya rika tofa alabarkacin bakin sa game da abinda ya faru.

Da dama da suma hada da majalisar tarayya da na Dattawa sun bayyana cewa Buhari bai bi doka ba wajen dakatar da Onnoghen.

Shima dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa Buhari ya yi amfani da darussan yadda ake karya doka daga ubangidan sa tsohon shugaban kasa Sani Abacha.

Atiku ya ce Buhari ya karya dokar kasa ce karara abin da yayi inda yayi kira ga ‘yan Najeriya da su tashi tsaye wajen nuna rashin amincewar su ga hakan.

Sai dai kuma tuni shugaba Buhari ya nada sabon mai shari’a, Mohammed Ibrahim, sannan ko waiwaya ba yayi ga duk ire-iren korafe-korafen da ake ta yi bisa abin da ya aikata.

Share.

game da Author