Onnoghen dan kasa ne kamar kowa, ya karya doka dole a hukunta shi

0

Idan ba a manta ba, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi yana kasar Nijar a wajen halartar taro, shugaban kasa na wancan lokaci, Goodluck Jonathan ya tsige shi.

Alkalai da dama sun yi ta tofa albarkacin bakin su bisa wannan aika-aika da gwamnatin lokacin ta yi.

Wasu daga cikin Alkalan na ganin cewa shugaban kasa Jonathan ba shi da daman tsige gwamnan babban bankin kasa ba tare da ya bi wasu sharudda da dokar kasa ta gindaya da suka hada da dole majalisar dattawa ta san da haka sannan kuma sai an tabbatar ya aikata laifin da ya zama dole ayi masa haka.

Jonathan ya dage cewa shima doka ta bashi wannan dama da zai iya tsige gwamnan babban bankin kasa a lokacin.

Haka dai aka yi ta yi inda daga karshe dai ya tabbata an tsige shi.

Babban mai shari’a na Najeriya Walter Onnoghen shima bata sake zani ba sai dai banbancin na sa shine an tabbatar da cewa ya tafka kuskure da shi da kansa ya ambata cewa yayi.

Dalilin da ya sa shugaba Buhari ya dakatar da shi shine domin a samu daman iya bincikar sa da kuma ya iya kare kan sa a gaban kotun da’ar ma’aikata, wato CCT.

Sai dai tun kafin Buhari ya aikata hakan gwamnonin yankin Kudu Maso Kudu suka rika ganawa suna fitar da bayanai cewa ba za su yarda da cin mutuncin da ake neman a yi wa mai shari’a Onnoghen ba.

Shima mataimakin shugaban kasa a lokacin milkin Olusegun Obasanjo kuma dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa Atiku Abubakar ya yi tir da abin da aka yi wa Onnoghen cewa hakan mulkin kama karya ne.

Abinda zai baka mamaki shine har zuwa yanzu babu wanda ya fito ya wage bakin sa domin kira ga Onnoghen ya sauka daga kujerar babban mai shari’a bisa abubuwan da ba zargi ba kawai shi da kan sa ya ambata yayi. Sannan kuma da gano ire-iren kadarori irin na gaba-gadi da ya mallaka ba bisa ka-ida ba sannan ya boye su domin kada yan kasa su sani.

An fi wage baki ne wajen ganin abinda aka yi masa ba daidai bane duk da ya tabbata shima ya waswaske da kudaden kasa.

Ko da yake akwai tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi amfani da duk irin daman da dokar kasa ta bashi ne wajen dakatar da shi Onnoghen amma dai wasu idanun su har yanzu a rufe suka saboda siyasa.

Share.

game da Author