Mace da ke takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar ACPC, Oby Ezekwesili ta janye daga takarar shugaban kasa.
A cikin wata sanarwa da ta watsa a shafin ta na twitter a safiyar yau Alhamis, ta ce ta janye daga takarar ne domin ta gina gagarimar gamayyar wayar wa jama’a kai ta yadda za a guji jam’iyyu biyu din nan masu karfi, wato APC da PDP a lokacin zabe, har a kayar da su.
Oby ta ce ta yi tunanin daukar wannan mataki ne biyo bayan abubuwan da suka wakana yayin makabalar da yi tare da wasu ’yan takarar shugabancin kasa a makon da ya gabata.
Ta ce akwai bukatar a wayar wa ‘yan Najeriya kai cewa ba fa za a iya ci gaba ba, har sai an kawar da gungun ‘yan jam’iyyar APC da PDP.
Kakakin yada labarai na Oby, mai suna Ozioma Ubabukoh, ya tabbatar da janyewar da Oby ta yi.
Discussion about this post