Shahararren mawakin Kannywood, Nura M Inuwa ya saki sabuwar waka wa dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.
Wannan waka da yayi wa taken ‘Lema ta Dinke’ tuni dai har ta karade kwararo-kwararo, lungu-lungu na Arewacin Najeriya.
A wakar Nura ya yabi Atiku da jam’iyyar PDP sannan da jinjina mata bisa dinkewa da tayi bayan barakar da ta fada a baya.
Haka nan shima fitaccen dan wasa kuma mawaki Sani Danja ya fidda sabuwar Bidiyo domin ci gaba da tallata gwanin su, wato Atiku Abubakar.
Kamar yadda a bangaren PDP din mawaka a Kannywood ke nuna kwazo da basirar su, haka suma wadanda jam’iyyar APC suke yi suke ta zuba wakoki domin wasa gwanin su wato Buhari da Jam’iyyar sa ta APC.