Neymar ya sake kwantawa jiyyar sabon rauni a kafar sa

0

Dan wasan PSG Neymar, ya fita daga cikin fili ya na kuka tare da dingishi bayan an ji masa ciwo a wasan da PSG ta yi nasara a kan Strasbourg.

Wasan dai na cin kofin Parisia ne, kuma PSG ta yi nasara da ci 2:0.

Da dama su na fargabar cewa raunin ya yi tsananin, ganin yadda ya rika kuka da kuma dingisa kafa.

Dan wasan Strasbourg Moataz Zemzemi ne ya yi ta harbin kafar Neymar har sau uku a kokarin sa na kwace kwallo daga kafar sa.

Hakan ya fusata Neymar, inda bayan alkalin wasa ya hura cewa an yi wa Neymar din keta, sai ya dauki kwallon ya buga ta a kam Zemzemi, wanda ya yi masa ketar.

Bayan an ci gaba da wasa, Neymar ya fita ya na dingishi, daga baya kuma ya sake komawa cikin fili da aka buba masa kafar.

Amma kuma ba da jimawa ba, ya sake dingisawa ya fice, aka sako Moussa Diaby a madadin sa a daidai minti na 62.

Share.

game da Author