Gwamnatin tarayya ta bada umarnin a rufe dukkan jami’o’in da ba su da cikakkar rijistar amincewa daga daga gwamnatida ke dukkan fadin kasar nan.
Ministan Ilmi, Adamu Adamu ne ya bada wannan sanarwar a taron da yay i da manema labarai a ranar Asabar da gabata, a Abuja.
Ya ce wadannan jami’o’i da manyan makarantu su na kawo wa tsarin ilmi koma-baya kuma su na karya darajar sa da ingancin sa a cikin kasar nan.
“Saboda ba su da takamaimen yawan daliban da su ke dauka, su na koyar da kwasa-kwasai wadanda ba a amince ko aka tantance cewa su koyar ba, kuma sau da yawa koyarwar da su ke yi wa dalibai duk birgi-birgi sallar kura su ke yi.”
Ya kuma yi korafin cewa yawan su ya na kara daburta aikin hukumar kula da jami’o’i sannan kuma ba su biyar harajin da ya kamata su rika biyan gwamnatin tarayya. Kuma ba su bin ka’idoji da dokoki.
Ya yi korafin cewa wasu jami’o’in ko manyan makarantun su na ribbatar dalibai ne ta hanyar buga cewa su na da hadin-guiwa da wasu manyan makarantu na kasahen Turai ko Afrika, wadanda a kasar nan ba a ma san su ba, kuma ba a amince ko tantance irin kwasa-kwasan da suke koyarwa ba.
Cikin 2018, PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Hukumar Kula Da Jami’o’i ta Kasa, NUC, ta ce akwai jami’o’i 58 da aka kafa ba bisa ka’ida ba a fadinn kasar nan.