Wasu matasa maza da mata tare da hadin guiwar bayan wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun yi kira ga gwamnati kan ta rage farashin audugan da mata kan yi amfani da su a lokacin da suke jini na wata-wata ganin cewa audugan yanzu yayi tsadan da yakan gagari mata siya domin amfani da shi.
Matasan sun gudanar da tattaki tare da aikawa da sakonni ta yanar gizo domin wayar da kan mutane game da illar dake tattare da tsadan farashin audugan mata ga matan kasar nan.
A kiran da suka yi matasan sun bayyana cewa a dalilin rashin iya siyan audugan da dama daga cikin mata sukan yi amfani ne da tsumokara wanda hakan ke cutar da lafiyar su.
” Idan har za a iya raba kwaroro roba kyauta domin kare mutane daga kamuwa da cututtuka irin na sanyi da kanjamau kamata yayi a rage ko kuma a raba wa mata auduga kyauta a kasar nan.
A ganawar da Wakiliyar PREMIUM TIMES ta yi da wasu ta gano cewa da yawa daga cikin mata yanzu tsummokara sukan nada su toshe gaban su idan suna haila saboda tsadar audugan da kuma talauci da yayi wa mutane katutu.
Gloria Dominic dalibar makarantar sakandare ne dake garin Abuja, ta bayyana cewa a dalilin tsadar da audugan ya yi takan yi amfani da tsumokara ne a duk lokacin da jini ya zo mata.
” Na gwamnace na yi amfani da kudin da zan kashe wajen siyan audugan duk wata a wani abin da zai fishe ne da rika cacan kudi wajen siyan audugan domin yayi matukar tsada a gani na. A dalilin haka da ni da sauran kanne ne mata muke amfani da tsuma abin mu domin bamu da lalin rika siyan audugan.
Hakan shine babban dalilin kiraye-kirayen da kungiyoyi ke yi wa gwamnatin Najeriya da ta maida hankali wajen tallafawa mara sa karfi musammam wajen ganin an rage kudin wannan auduga ko don kiwon lafiyar mata a kasar nan.
Abinda likitoci suke cewa
Likitan mata kuma ma’aikacin asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan Imran Morhason-Bello ya bayyana cewa amfani da tsumma ko kuma auduga musamman wadanda ba a sarrafa shi ba domin haila na cutar da lafiyar mata.
Ya ce rashin yin amfani da audugan yin hailan da ya kamata na iya kawo wa mace munanan cututtuka wanda ka iya yin ajalinta ma.
” A dalilin haka nake kira ga mata da su daure su rika amfani da audugan da ya kamata domin guje wa matsalolin da ka iya cutar da kiwon lafiyar su.
A karshe jagoran matasa Harvey Olufunmilayo da shugaban kungiya mai zaman kanta ‘Whole Woman Network’, Juliet Kego sun yi kira ga gwamnati kan rage farashin audugan domin ceto rayukan matan kasar nan.
Discussion about this post