MAZA AYI HATTARA: Wani ya ya kamu da cutar makancewar dare a dalilin shan maganin kara karfin gaba

0

Wasu likitocin asibitin kula da kunne da ido dake Massachusetts, Boston kasar Amurka sun bayyana cewa wani magidanci ya makance a dalilin shan maganin kara karfin gaban sa.

Wannan magidancin wanda shekarunsa ba zai gaza 50 ba ya kwankwadi wannan ruwan magani mai suna ‘Liquid Sildenafil’ sau goma fiye da yadda ya kamata domin ganin ya rabu da wannan matsalar rashin karfin gaba da yake fama da shi.

Likitocin sun ce a dalilin haka ya kamu da cutar makanta da ake kira ‘Night Blindness’ sannan kuma rudewa.

‘‘Makantar Night Blindness makan ce da mutum ke rasa iya ganin da zaran duhu yayi.

Likitocin sun ce bayan aiki da akayi a kan sa ya sami sauki matuka sai dai yananan a rude, baya gane gaban sa ballantana yayi aikata wani abu mai ma’na duk saboda wannan ganganci da yayi.

A karshe likitocin sun yi kira ga maza da su guji shan maganin kara karfin gaba fiye da yadda ya kamata sannan ba tare da izinin likita ba domin haka na iya cutar da lafiya su.

Share.

game da Author