Mawallafin PREMIUM TIMES, Dapo Olorunyomi, gode wa daukacin dimbin masu karanta jaridar ta sa dangane da gagarimin goyon bayan da suke bayarwa tare da karin kwarin gwiwa.
Dapo kuma ya hori ma’aikatan sa su tsaya kan turbar ka’idojin aikin jarida.
Dukkan wadannan godiya da gargadi su na kunshe ne a cikin Sakon Murnar Shiga Sabuwar Shekara ta 2019 da wannan mashahuri kuma gogaggen dan jarida ya yi wa masu karatu da ma’aikatan sa.
Mawallafin wanda ya sha karbar kyaututtukan yabo da gwarzantawa a fannin aikin jarida a ciki da wajen kasar nan, ya jaddada cewa PREMIUM TIMES za ta ci gaba da kasancewa babban makamin karfafa turbar dimokradiyya da kuma kakakin busa busharar tabbatar da ana mulki mai inganci a karkashin ita kan ta dimokradiyyar da ake son ingantawa.
Ya kuma kara tabbatar da cewa PREMIUM TIMES ba za ta taba kaucewa daga matsayin ta na bulalar sake karkato da daidaiton tsari da ingancin gwamnati ba.
“Ba don ku masu karatu ba, da jaridar ba ta kawo a yadda ta ke a yanzu ba. Sannan matsawar mu na tare da ku, to mu kuma mu na kara tabbatar muku da cewa za mu kara kaimi da hobbasa domin tabbatar da cewa mu na ci gaba da bin hanya da turbar da mu ke a kai tun da farko, wato turba ta bin ka’idar aikin jarida, gogewa da nuna kwarewa a kan aikin mu da ka’idojin aikin jarida ya shimfida.”
An kafa PREMIUM TIMES a Abuja shekaru takwas da suka gabata, inda cikin kankanen lokaci ta rika lashe manyan kyaututtukan yabon kwarewa da iya binciken kwakwaf na aikin jarida a cikin Najeriya a fadin kasashen duniya.