Mataimakin Shugaban PDP na Arewa da aka dakatar ya koma APC

0

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Arewa, Babayo Gamawa da aka dakatar a shekaranjiya, ya koma jam’iyyyar APC a jiya Talata.

An dakatar da Gamawa saboda zargin sa da sakaci da aiki da kuma yi wa PDP yankan-baya, wato ‘anti’party’.

Kakakin Yada Labaran Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina ne ya bayyana sanarwar komawar Babayo APC.

Adesina ya tura hotunan Gamawa tare da Buhari da gwamnan Bauchi, Mohammed Abubakar, a lokacin da suka kai ziyara gidan shugaba Buhari.

Tare da su akwai Hon. Aliyu Kaulaha a cikin hoton da suka dauka da Buhari da kuma gwamna Abubakar na Buachi.

Share.

game da Author