Masu fama da cutar Kanjamau na biyan Naira 2000 kudin maganin – NEPWHAN

0

Hadaddiyar kungiyar masu dauke da cutar kanjamau (NEPWHAN) ta koka kan yadda mamobinta masu dauke da wannan cuta ke biyan Naira 2000 duk wata domin samun maganin cutar a kasar nan.

Jami’in kungiyar reshen jihar Legas Peter Obialor ne ya koka kan haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a makon da ya gabata a Legas.

Obialor yace a dalilin haka da dama daga cikin wadanda ke fama da cutar dake basu iya samun magani.

” Sannan wani abin takaici shine hatta yin gwaji sai mambobin mu sun biya da haka bai kamata ba.

Obialor ya ce a dalilin haka ne yake kira ga gwamnati data gaggauta daukan mataki don hana hakan ci gaba da faruwa ganin cewa hakan na iya kawo koma baya wajen a kokarin da ake yi na kawar da cutar daga nan zuwa shekarar 2030 da gwamnati ke kokarin ganin ya tabbata.

A karshe ya kuma yi kira ga gwamnati da inganta aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko domin samar da kula wa masu dauke da cutar a fadin kasar nan.

” Yin hakan zai taimaka wajen inganta matakan da gwamnati ta tsara domin dakile yaduwar cutar musamman yadda cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ne suka fi kusa da mutane.”

Share.

game da Author