A yau Litini ne makarantar sakandare mallakar jami’ar LAUTECH dake Ogbomoso jihar Oyo ta hana wasu dalibai mata 55 shiga ajujuwan su saboda sun saka hijabi.
Wani malami a makarantar da baya so a fadi sunansa ya bayyana haka wa manema labarai yana mai cewa tun daga kofar shiga makarantar aka fara koran duk dalibar da ta saka hijabi ta zo makaranta.
” Iyaye da kungiyoyin musulunci sun rubuta wasika ga hukumar makarantar nan da ta bari dalibai mata su rika saka hijabi idan za su zo makaranta amma har yanzu hukumar ta ce bata kammala yin nazari a kai ba.
Malamin ya ce dalilin gajiyar jiran hukuncin da hukumar makarantar za ta dauka ne ya sa iyayen wadannan dalibai suka bari yaran su su ka suka saka hijabin kai tsaye kawai suka turo su makaranta wanda a dalilin haka kuwa a kora su gida.
A karshe shugaban makarantar Ibrahim Animashaun ya yi kira ga iyaye da su kara yin hakuri su jira hukumar makarantar ta yanke hukunci bisa ga bukatar su.
” Ina tabbatar muku da cewa da zarar mahukuntar makarantar nan sun kammala yin nazari kan wannan batu za a sanar da iyaye amma a yanzu haka ina kira ga iyaye da dalibai mata da su dakatar da saka hijabi zuwa makaranta.