Majalisar Wakilai ta tarayya ta amince da kudirin kankantar Albashi na naira 27,000

0

A yau Talata ne shugaban majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya tabbatar wa ‘yan uwansa a majalisar da ‘yan Najeriya cewa tuni dai ya koma jam’iyyarsa ta da wato jam’iyyar PDP.

Tare da Dogara akwai Dan majalisar Ahmed Yerima da Pwajok wanda duk ‘yan jam’iyyar APC ne sun koma PDP suma.

Bayan haka majalisar ta amince da kudirin Karin kankantar Albashi ma’aikatan Najeriya daga naira 17,000 zuwa naira 27,000 Kamar yadda Buhari ya mika wa majalisar.

Yanzu idan majalisar dattawa ta dawo daga hutu bayan Zabe za ta tattauna batun domin amincewa da shi.

Idan ba a manta ba anyi ta Kai ruwa rana tsakanin kungiyar kwadago da fadar gwamnati inda kungiyar ta rika zazzaro idanu tana cewa ba zata amince da naira 27,000 a matsayin kankantar albashin ma’aikacin gwamnati a kasar nan ba.

Hakan dai ta Kai ga kungiyar ta yi barazanar fara yajin aikin gama gari idan ba a amince da naira da 30,000 ba.

Sai dai kuma tun bayan zaman da kwamitin kasa ta yi inda ta amince da naira 27,000 Buhari ya mika wa majalisar dokoki ta Kasa domin amincewa da.

A baya-bayan nan kungiyar Gwamnonin kasar nan karkashin jagorancin AbdulAziz Yari na Jihar Zamfara, ta yi Kira ga majalisar Kasa din da Kasa ta saka hannu a kudirin cewa gwamnatocin jihohi ba za su iya biyan 30,000 karancin Albashi.

Share.

game da Author