Majalisar Dattawa za ta dawo daga hutu domin yin muhawara game da dakatar da Onnoghen

0

Majalisar Dattawa na kokarin sake bude majalisar cikin makon gobe, domin ta dawo daga hutu yadda dattawa za su murza gashin baki.

Hakan ya biyo bayan dakatar da Cif Jojin Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, ba tare da tuntubar majalisar ba, kuma ya nada wani sabo.

Wani Sanata ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa tabbas an anko masa sakon tes na kar-ta-kwana cewa za a koma majalisa cikin makon gobe, domin a dauki kwakkwaran matsayi dangane da dakatar da Walter Onnoghen da Buhari ya yi, ya nada Tanko Mohammed a madadin sa.

Ya ce ba shi kadai aka tura wa sakon ba, wanda ke dauke da cewa kowa ya halarci zaman majalisa a ranar Talata.

Sanatan ya ce babbar ajandar zaman da za su yi shi ne su bijire wa abin da ya kira ” danyen hukuncin da Shugaba Buhari ya aikata.”

“Manufar batun shi ne a yi amfani dukkan sanatocin da ba ‘yan APC ba a samu kwakwarar matsayar da za a fitar da sanarwa ga Buhari da ma duniya baki daya.”

Daya daga cikin matakan da za su dauka shi ne yin amfani da Sashe na 143 na Dokar Kasa su shigo da batun tsige Shugaba Buhari.

Sai dai kuma Kakakin Yada Labarai na Saraki, Yusuf Olaniyonu ya ce bai san da zancen komawar sanatacin majalisa ba.

Share.

game da Author