Idan ba a manta ba a watan Disamba ne masu garkuwa sun yi garkuwa da wasu ‘yan agaji 20 a hanyar su na dawowa daga aikin jinkai a Zamfara.
An sace wadannan ‘yan agaji ne ranar 23 ga watan Disamba.
Sani Jingir da ya sanar da haka ga manema Labarai a garin Jos ya bayyana cewa an saki wadannan ‘yan agaji ne ba tare da an biya kudin diyya ba.
” An sako su a garin Dauran dake karamar hukumar Zurmi, jihar Zamfara sannan ba a biya ko sisi ba. Wadannan ‘Yan agaji na cikin koshin lafiya.
Jingir ya godewa wadanda suka yi ta yin fadi tashi wajen ganin an ceto wadannan ‘yan agaji.
Discussion about this post